Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 5:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun 'ya'yansa ne.

2. Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.

3. Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.

4. Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.

5. Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.

Karanta cikakken babi Afi 5