Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 5:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun 'ya'yansa ne.

2. Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.

3. Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.

4. Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.

5. Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.

6. Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne fushin Allah yake aukawa a kan kangararru.

7. Saboda haka, kada ku yi cuɗanya da su,

8. domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,

9. domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.

10. Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji.

11. Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.

Karanta cikakken babi Afi 5