Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 4:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ba haka kuka koyi al'amarin Almasihu ba,

21. in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take.

22. Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha'awoyinsa na yaudara,

23. ku kuma sabunta ra'ayin hankalinku,

24. ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.

25. Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.

26. In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,

27. kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.

28. Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta.

29. Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.

Karanta cikakken babi Afi 4