Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 3:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,

9. in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa.

10. An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.

11. Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

12. A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi.

13. Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

14. Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban,

15. shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,

16. ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,

17. har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,

Karanta cikakken babi Afi 3