Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 3:17-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,

18. har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,

19. ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.

Karanta cikakken babi Afi 3