11. Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
12. A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi.
13. Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.
14. Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban,
15. shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,
16. ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,
17. har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,
18. har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,