Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai,

2. in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku,

3. wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice.

4. A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu,

5. wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,

6. wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.

7. An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.

8. Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,

9. in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa.

10. An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.

11. Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Karanta cikakken babi Afi 3