Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 2:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.

7. Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.

8. Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,

9. ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.

10. Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

11. Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

12. Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama'ar Isra'ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.

13. Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.

14. Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al'ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba.

Karanta cikakken babi Afi 2