Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 2:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kuma yā raya ku sa'ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku,

2. waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.

3. Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.

4. Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana,

5. ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),

6. a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.

7. Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.

8. Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,

9. ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.

10. Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

11. Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

Karanta cikakken babi Afi 2