Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 1:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.

10. Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.

11. A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,

12. domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa.

13. A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa'ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.

14. Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.

15. Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka,

16. ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa'ad da nake yi muku addu'a,

17. da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah,

18. a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,

19. da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa,

20. wanda ya zartar ga Almasihu sa'ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya,

Karanta cikakken babi Afi 1