Surori

  1. 1

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

3 Yah 1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Gaisuwa

1. Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.

2. Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.

3. Na yi farin ciki ƙwarai sa'ad da waɗansu 'yan'uwa suka zo suka shaida gaskiyarka, yadda hakika kake bin gaskiya.

4. Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji 'ya'yana suna bin gaskiya.

Yaba Kirkin Gayus

5. Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa 'yan'uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba.

6. Su ne suka shaida ƙaunarka a gaban ikkilisiya. Zai kyautu ka raka su a guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah,

7. domin saboda sunan nan ne suka fito, ba sa kuma karɓar kome daga al'ummai.

8. Domin haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, domin mu zama abokan aiki da su a kan gaskiya.

Diyotarifis Mai Ƙin Bin Magana

9. Na yi wa ikkilisiya 'yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu.

10. Saboda haka, in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa 'yan'uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fitar da su daga ikkilisiya.

Kyakkyawar Shaida kan Dimitiriyas

11. Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.

12. Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa, har gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.

Gaisuwa

13. Dā kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa.

14. Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.

15. Salama tă tabbata gare ku. Aminanmu suna gaishe ka. Ka gai da aminanmu kowa da kowa.