Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Yah 1:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna.

7. Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.

8. Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako.

9. Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.

10. Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa.

11. Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa, sai yă shafe shi.

12. Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke.

13. 'Ya'yan 'yar'uwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ki.

Karanta cikakken babi 2 Yah 1