Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Yah 1:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,

2. wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar da take a dawwame a cikinmu, za ta kuwa kasance tare da mu har abada.

3. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna.

4. Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu 'ya'yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni.

5. Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna.

6. Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna.

7. Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.

8. Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako.

9. Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.

10. Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa.

Karanta cikakken babi 2 Yah 1