Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 4:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,

2. ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.

3. Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.

4. Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.

5. Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.

6. Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato.

Karanta cikakken babi 2 Tim 4