Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 3:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta,

4. da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah,

5. suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.

6. A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,

7. kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya.

8. Kamar yadda Yanisu da Yambirisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma suke tayar wa gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu kuwa ta banza ce.

9. Amma ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

10. Kai kam, ka riga ka kiyaye koyarwata, da halina, da niyyata, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da jimirina,

11. da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka.

12. Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna ga Almasihu Yesu, za su sha tsanani.

13. Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.

14. Amma kai kuwa, ka zauna a kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su,

15. da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu.

16. Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,

17. domin bawan Allah yă zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.

Karanta cikakken babi 2 Tim 3