Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma ka fahimta, a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai.

2. Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka,

3. da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta,

4. da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah,

5. suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.

Karanta cikakken babi 2 Tim 3