Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 2:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.

4. Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha'anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja.

5. Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan.

6. Ma'aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.

7. Ka yi tunani a kan abin da nake faɗa, Ubangiji kuwa zai ba ka fahimtar kome.

8. Ka tuna da Yesu Almasihu fa, shi da aka tashe shi daga matattu, na zuriyar Dawuda bisa ga bisharata,

9. wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.

10. Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.

11. Maganar nan tabbatacciya ce,“In mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi,

12. In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi,In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,

13. In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,Domin ba zai yi musun kansa ba.”

14. Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

Karanta cikakken babi 2 Tim 2