Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 2:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.

3. Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.

4. Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha'anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja.

5. Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan.

6. Ma'aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.

Karanta cikakken babi 2 Tim 2