Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 2:16-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

17. maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas,

18. waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

19. Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”

20. A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na itace da na yumɓu, waɗansu don aikin ɗaukaka, waɗansu kuwa don ƙasƙantaccen aiki.

21. Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma'aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.

22. Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.

23. Ka ƙi gardandamin banza marasa ma'ana, ka san lalle suna jawo husuma.

24. Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri,

25. mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali'u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya,

26. su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.

Karanta cikakken babi 2 Tim 2