Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 1:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, don sanar da alkawarin nan na rai wanda yake ga Almasihu Yesu,

2. zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana.Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.

3. Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa.

4. Sa'ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa.

Karanta cikakken babi 2 Tim 1