Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tas 3:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi.

5. Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.

6. To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.

7. Ai, ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa'ad da muke a tare, ba mu nuna muku lalaci ba,

8. ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku.

9. Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a'a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu.

10. Ai, ko dā ma, sa'ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.

11. Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum.

12. To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu.

13. Amma ku 'yan'uwa, kada ku gaji da yin aiki nagari.

14. In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata.

15. Amma kada ku ɗauke shi a kan abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a kan shi ɗan'uwa ne.

16. To, Ubangiji kansa, mai zartar da salama, yă ba ku salama a koyaushe a kowane hali. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.

17. Ni Bulus, ni nake rubuto wannan Gaisuwa da hannuna. Ita ce kuwa shaidar kowace wasiƙata. Rubutun hannuna ke nan.

18. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka.

Karanta cikakken babi 2 Tas 3