Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tas 2:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.

5. Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare?

6. To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa.

7. Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna.

8. A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.

9. Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al'ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri,

10. yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.

11. Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya,

12. don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.

13. Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.

14. Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

Karanta cikakken babi 2 Tas 2