Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tas 1:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.

9. Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,

10. wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.

11. Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu'a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa,

12. don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.

Karanta cikakken babi 2 Tas 1