Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Gudunmawa ga Tsarkaka

1. Ba sai lalle na rubuto muku zancen gudunmawa ga tsarkaka ba,

2. domin na san niyyarku, har ma ina taƙama da ku gun mutanen Makidoniya a kan haka, ina ce musu Ikkilisiyar Akaya ta yi shiri tun bara, ƙwazonku kuwa ya ta da yawancinsu.

3. Amma ma aiko da 'yan'uwan nan, don kada gadarar da muke yi da ku a wannan al'amari ta zama banza, domin ku zauna a kan shiri, kamar yadda dā na ce za ku zauna.

4. Don kada ya zamana in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba ku shirya ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.

5. Saboda haka, na dai ga lalle ne in roƙi 'yan'uwan nan su riga ni zuwa a gare ku, su tanada baiwar nan da kuka yi alkawari kafin in zo, domin a same ta a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.

6. Abin la'akari fa, shi ne wanda ya yi ƙwauron yafa iri, gonarsa za ta yi masa ƙwauron amfani, wanda kuwa ya yafa a yalwace, sai ya girba a yalwace.

7. Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.

8. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

9. Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Ya ba gajiyayyu hannu sake,Ayyukansa na alheri madawwama ne.”

10. Shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, ya riɓanya shi, ya kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri.

11. Za a wadata ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa a yalwace, bayarwar nan kuwa da za ku yi, za ta zama sanadin godiya ga Allah ta wurinmu.

12. Domin aikin nan na alheri, ba biyan bukatar tsarkaka kaɗai yake yi ba, har ma yana ƙara yawaita godiya ga Allah ƙwarai da gaske.

13. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.

14. Su kuwa za su yi muku addu'a, su yi ɗokin ganinku saboda alherin Allah marar misaltuwa da ya yi muku.

15. Godiya tā tabbata ga Allah saboda baiwarsa da ta fi gaban a faɗa.