Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, 'yan'uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,

2. wato, ko da yake an gwada su da matsananciyar wahala, suna kuma a cikin baƙin talauci, duk da haka, yawan farin cikinsu, har ya kai su ga yin alheri ƙwarai da gaske.

3. Domin na tabbata daidai ƙarfinsu suka bayar, har ma fiye da ƙarfinsu ne, da ra'insu kuma.

4. Sun roƙe mu ƙwarai da gaske mu yi musu alheri su ma, a sa su a cikin masu yi wa tsarkaka gudunmawa,

5. har ma suka bayar fiye da yadda muka zata, amma sai da suka fara miƙa kansu ga Ubangiji da a gare mu kuma, bisa ga nufin Allah.

6. Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.

7. To, da yake kun fifita a kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da magana, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunar da kuke yi mana, to, sai ku fifita a wannan aikin alheri ma.

8. Ba kallafa muku wannan nake yi ba, sai dai ta nuna himmar waɗansu, in tabbata ƙaunarku ma sahihiya ce.

9. Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.

10. A wannan al'amari, ga shawarata. Ai, ya fiye muku a yanzu ku ƙarasa abin da kuka fara yi a bara, har kuka yi da ra'inku.

11. To, sai ku ƙarasa aikin da irin ra'in da kuka fara, gwargwadon ikonku.

12. Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

Karanta cikakken babi 2 Kor 8