Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 6:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Domin ya ce,“Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa,Na kuma taimake ka a ranar ceto.”Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!

3. Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,

4. Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,

5. da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.

6. Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar ƙauna,

7. da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.

8. Ana ɗaukaka mu, ana kuma wulakanta mu, ana yabonmu, ana kuma kushenmu. An ɗauke mu kamar mayaudara, mu kuwa masu gaskiya ne.

9. Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa, muna a raye, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba,

Karanta cikakken babi 2 Kor 6