Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 5:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama.

2. A jikin nan muna ajiyar zuciya, mun ƙosa mu samu a suturta mu da jiki namu na Sama,

3. gama in aka suturta mu da shi, ba za a same mu tsirara ba.

4. Sa'ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.

5. Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewar, shi da ya ba mu Ruhunsa, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.

6. Saboda haka, kullum muke da ƙarfin zuciya, mun kuma sani, muddin muna tare da wannan jiki, a rabe muke da Ubangiji,

7. domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba.

8. Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji.

Karanta cikakken babi 2 Kor 5