Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 11:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.

4. Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!

5. A ganina ban kasa mafifitan manzannin nan da kome ba.

6. Ko da yake ni bāmi ne a wajen yin magana, a wajen sani kam, ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya a cikin dukan sha'aninmu da ku.

7. Ashe, laifi na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaukaka ku, wato, saboda na yi muku bisharar Allah a kyauta?

8. Waɗansu ikilisiyoyi na biyan hakkina, sai ka ce ina yi musu ƙwace domin in yi muku hidima.

9. Sa'ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin 'yan'uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.

10. Albarkacin gaskiyar Almasihu da yake tare da ni, ba mai hana ni fahariyar nan tawa a lardin Akaya.

11. To, don me? Domin ba na ƙaunarku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku.

12. Abin da nake yi kuwa, shi zan riƙa yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.

13. Irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, mayaudaran ma'aikata, suna mai da kansu kamar su manzannin Almasihu ne.

14. Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa, yakan mai da kansa kamar shi mala'ikan haske ne.

15. Don haka, ba abin mamaki ba ne in bayinsa ma sun mai da kansu kamar su bayi ne na aikin adalci. A ƙarshe za a saka musu gwargwadon ayyukansu.

Karanta cikakken babi 2 Kor 11