Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 11:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ma a ce ku jure 'yar wautata. Ku dai yi haƙuri da ni!

2. Ina kishi a kanku saboda Allah. Gama na bashe ku ga Almasihu, domin in miƙa ku kamar amarya tsattsarka ga makaɗaicin mijinta.

3. Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.

4. Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!

5. A ganina ban kasa mafifitan manzannin nan da kome ba.

6. Ko da yake ni bāmi ne a wajen yin magana, a wajen sani kam, ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya a cikin dukan sha'aninmu da ku.

7. Ashe, laifi na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaukaka ku, wato, saboda na yi muku bisharar Allah a kyauta?

8. Waɗansu ikilisiyoyi na biyan hakkina, sai ka ce ina yi musu ƙwace domin in yi muku hidima.

9. Sa'ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin 'yan'uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.

10. Albarkacin gaskiyar Almasihu da yake tare da ni, ba mai hana ni fahariyar nan tawa a lardin Akaya.

11. To, don me? Domin ba na ƙaunarku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku.

Karanta cikakken babi 2 Kor 11