Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 10:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba.

9. Kada fa a ga kamar ina tsorata ku da wasiƙu ne.

10. Don waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.”

11. Irin mutanen nan dai su fahimci yadda abin da muke faɗa a cikin wasiƙa sa'ad da ba ma nan, shi muke aikatawa sa'ad da muke nan.

12. Wane mu mu daidaita kanmu, ko mu gwada kanmu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe, waɗannan mutane masu auna kansu da juna, suna kuma neman bambanci a tsakaninsu da juna, ba su da basira.

13. Amma dai ba za mu yi alfarma fiye da yadda ya kamata ba, sai dai mu tsaya a kan iyakar da Allah ya yanke mana, wadda ta game har da ku.

14. Ai, ba mu wuce gona da iri ba, kamar ba a hannunmu kuke ba, domin mu ne muka fara shan nisa, muka je a gare ku da bisharar Almasihu.

15. Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba ta kuma shafi aikin waɗansu ba. Amma muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku ya riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske,

16. har ma mu samu mu yi bishara a ƙasashen da suke a gaba da ku, ba tare da wata fahariya da aikin da wani ya riga ya yi a fagensa ba.

17. Amma, “Duk mai yin fahariya, ya yi fahariya da Ubangiji.”

18. Ai, ba mai yabon kansa ake yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

Karanta cikakken babi 2 Kor 10