Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 3:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.

9. Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.

10. Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.

11. Tun da yake duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada,

12. kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su hallaka, dukkan abubuwa kuma da suke a cikinsu, wuta za ta narkar da su.

13. Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin summai da sabuwar ƙasa a inda adalci zai yi zamansa.

14. Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama.

15. Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan'uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,

16. yana magana a kan wannan, kamar yadda yake yi a dukan wasiƙunsa, akwai waɗansu abubuwa a cikin masu wuyar fahinta, waɗanda jahilai da marasa kintsuwa suke juya ma'anarsu, kamar yadda suke juya sauren Littattafai, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

17. Don haka, ya ku ƙaunatatuna, da yake kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.

18. Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!

Karanta cikakken babi 2 Bit 3