Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 3:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakar da sahihan zukatanku ta hanyar tuni.

2. Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.

3. Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,

4. suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”

5. Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.

6. Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.

7. Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.

8. Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.

Karanta cikakken babi 2 Bit 3