Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 2:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.

16. Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana kamar mutum, ta kwaɓi haukan annabin nan.

17. Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.

18. Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,

19. suna yi musu alkawarin 'yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi.

20. In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.

21. Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.

22. Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”

Karanta cikakken babi 2 Bit 2