Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 2:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.

2. Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.

3. Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.

4. Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,

5. tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,

6. da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,

Karanta cikakken babi 2 Bit 2