Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 1:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.

2. Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu

3. Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa,

4. waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa.

5. Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata,

6. sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah,

7. bin Allah da son 'yan'uwa, son 'yan'uwa kuma da ƙauna.

8. In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

9. Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā.

10. Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.

Karanta cikakken babi 2 Bit 1