Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 4:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.

6. Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.

7. Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.

8. Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna.

9. Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.

10. Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.

11. Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.

12. Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama cikinmu, ƙaunar nan tasa kuma tă cika a cikinmu.

Karanta cikakken babi 1 Yah 4