Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 4:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

2. Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.

3. Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya.

4. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.

5. Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.

6. Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.

7. Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.

8. Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna.

9. Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.

10. Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.

11. Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.

Karanta cikakken babi 1 Yah 4