Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 3:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.

9. Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.

10. Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.

11. Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna,

12. kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.

13. Kada ku yi mamaki, 'yan'uwa, idan duniya take ƙinku.

14. Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar 'yan'uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi.

15. Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi.

16. Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa.

17. Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?

18. Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.

Karanta cikakken babi 1 Yah 3