Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 6:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Duk ɗaukacin masu igiyar bauta a wuyansu, su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwar nan.

2. Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su.Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.

3. Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,

4. girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace,

5. da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.

6. Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.

7. Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.

8. To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.

Karanta cikakken babi 1 Tim 6