Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 5:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al'amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa'azi da koyarwa ba.

18. Domin Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa'ad da yake sussuka.” Ya kuma ce, “Ma'aikaci ya cancanci ladarsa.”

19. Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikkilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku.

20. Masu yin zunubi kuwa, sai ka tsawata musu a gaban dukkan jama'a, don saura su tsorata.

21. Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.

22. Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.

23. A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.

24. Zunuban waɗansu mutane a fili suke, tun ba a kai gaban shari'a ba. Zunuban waɗansu kuwa, sai daga baya suke bayyana.

25. Haka kuma, kyawawan ayyukan waɗansu a fili suke, waɗanda ba haka suke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.

Karanta cikakken babi 1 Tim 5