Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 4:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,

2. ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas.

3. Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.

4. Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya,

5. gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu'a

6. In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau.

7. Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah.

8. Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.

9. Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum.

10. Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.

11. Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su.

12. Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka.

Karanta cikakken babi 1 Tim 4