Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 2:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu'ulu'u, ko tufafi masu tsada ba,

10. sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu.

11. Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.

12. Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.

13. Ai, Adamu aka fara halitta, sa'an nan Hawwa'u.

14. Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni.

15. Duk da haka kuwa, ta wurin haifar 'ya'ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.

Karanta cikakken babi 1 Tim 2