Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 2:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu'a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane,

2. da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.

3. Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,

4. wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.

5. Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,

Karanta cikakken babi 1 Tim 2