Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 5:11-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.

12. Amma muna roƙonku 'yan'uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi.

13. Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.

14. Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.

15. Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.

16. Ku riƙa yin farin ciki a kullum.

17. Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa.

18. Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.

19. Kada ku danne maganar Ruhu.

20. Kada ku raina annabci,

21. sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan.

22. Ku yi nesa da kowace irin mugunta.

23. Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

24. Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25. Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.

26. Ku gai da dukkan 'yan'uwa da tsattsarkar sumba.

27. Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan 'yan'uwa wasiƙar nan.

Karanta cikakken babi 1 Tas 5