Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 4:3-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,

4. kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,

5. ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.

6. A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.

7. Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne.

8. Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

9. A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.

10. Hakika kuwa kuna ƙaunar dukan 'yan'uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,

11. kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha'anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku,

12. domin ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.

13. Amma 'yan'uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege.

Karanta cikakken babi 1 Tas 4