Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu.Alheri da salama su tabbata a gare ku.

2. A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu'armu,

3. ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.

4. Domin mun sani, 'yan'uwa, ƙaunatattu na Allah, shi ya zaɓe ku,

5. domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,

Karanta cikakken babi 1 Tas 1