Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 4:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.

6. To, 'yan'uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani.

7. Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?

8. Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!

9. Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.

10. An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!

11. Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.

12. Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.

13. In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

Karanta cikakken babi 1 Kor 4