Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 4:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah.

2. Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce.

3. A gare ni kam, sassauƙan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ma ba na gwada kaina.

4. Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.

5. Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.

6. To, 'yan'uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani.

7. Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?

8. Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!

9. Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.

10. An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!

Karanta cikakken babi 1 Kor 4