Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 3:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.

11. Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu.

12. To, kowa ya yi ɗori da zinariya a kan harsashin nan, ko da azurfa, ko da duwatsun alfarma, ko da itace, ko da shuci, ko da kara,

13. ai, aikin kowane mutum zai bayyana, domin ranar nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa.

14. In aikin da kowane mutum ya ɗora a kan harsashin nan ya tsira, to, zai sami sakamako.

15. In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai yă yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.

Karanta cikakken babi 1 Kor 3