Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma ni, 'yan'uwa, ban iya yi muku jawabi ba, kamar yadda nake yi wa mutanen da suke na ruhu, sai dai kamar yadda nake yi wa masu halin mutuntaka, kamar jarirai a cikin bin Almasihu.

2. Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba,

3. don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka?

4. Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afolos ne,” ashe, ba aikata halin mutuntaka kuke yi ba?

5. To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?

6. Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar.

7. Don haka da mai shukar, da mai banruwan, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar.

8. Da mai shukar, da mai banruwan, duk daidai suke, sai dai ko wanne zai sami tasa ladar gwargwadon wahalarsa,

9. gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10. Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.

11. Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 3